Ban taba ganin Dan ta’addan daya sami Gwamnati kamar Ganduje ba Dan ta’adda ne na karshe na Gani da ido na a wannan zaben ~Cewar Kwankwaso.

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso Yana wannan jawabi ne a lokacin da ‘yan Kasuwar jihar Kano suka Kai Masa ziyarar taya murna bisa lashen zaben Gwamnan jihar Kano da Engr Abba Kabir Yusuf bisa jagorancin Kwankwasiyya yayi a ranar Asabar data gudana.
A lokacin jawabin sa Sanata Rabi’u Kwankwaso Yana jabi irin yadda Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Ganduje ta koma da Kano baya.
Yana Mai cewa duk wani Ayyukan Alkhairi da ya kafa kafin ya bar Gwamnati a yanzu Ganduje ya rushehi ya lalatashi, wannan Dan dabar shi Kansa ban taba ganin Dan ta’adda ya sami Gwamnati kamar Ganduje ba Dan ta’adda ne na karshe na Ga wannan da ido na a wannan zaben ya ha’da Yan Daba ko yau ya ha’da Daba Sunan can suna zanga zanga, zanga-zangar banza in Kaci zabe Kaci zabe idan baka ci zabe ba baka ci ba.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso wannan jawabin sa na farko wanda ha ja hankali tun bayan lashe zaben da Engr Abba Kabir Yusuf yayi a jihar kano.