Ban taba ganin Gwamnati Mara Imani da Tausayi Irin Gwamnatin Shugaba Buhari ba, Salihu Tanko Yakasai
Mashawarci na Musamman ga Gwamna Abdullahi Ganduje kan harkokin yada labarai, Salihu Yakasai, ya ce Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ba shi da tausayin ’yan Najeriya. Yakasai, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, @dawisu, yana mai da martani ne kan gazawar Shugaban kasa na yin jawabi ga ’yan Najeriya a yayin fushin yan kasa gami da ci gaba da zanga-zangar da ake yi Kan Yan Sandan SARS mai taimaka wa gwamnan ya dage cewa Buhari ya nuna halin ko-in-kula ta yadda bai yi wayan kasar jawabi ba. Yakasai ya rubuta, “Ban taba ganin gwamnatin da ba ta da tausayi irin ta Shugaba Muhammadu Buhari ba.
“Sau da yawa lokacin da jama’arsa ke cikin wani mawuyacin hali kuma suna tsammanin wani irin taimako zai kawo garesu do tabbatar musu da cewa shi ke kan mulki, kunje jihohi 36 don neman kuri’un talakawa abin takaici ne.” Dubun-dubatar matasan Najeriya sun yi zanga-zangar Kan cin zarafin ‘yan sanda da kashe-kashe ba tare da shari’a ba da SARS, sama da shekaru goma da suka gabata don magance fashi da makami aka Samar da da SARS Amma, tsawon shekarun Babu abinda jami’an SARS sukeyi sai karbar kudi daga samarin da ke tuka manyan motoci, da wayoyi masu tsada, kwamfutar tafi-da-gidanka ko kuma sanya takunkumi. Tursasawar a lokuta daban-daban ta rikide zuwa kashe-kashe. Inji Salihu Tanko Yakasai.
Sabuwar zanga-zangar wacce aka faro ta ranar Alhamis, ta samu karbuwa daga masu nishadantarwa na cikin gida da na waje da kuma wasu fitattun mutane da dama ciki har da ‘yar Shugaban kasa, Zahra Buhari-Indimi; kazalika diyar Mataimakin Shugaban Kasa, Kiki Osinbajo.