Ban taba satar kudin gwamnati ba – El-Rufai
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya kalubalanci magabatansa a jihar da su fito su yi rantsuwar cewa ba su taba satar dukiyar jihar ba.
Ya ce a wata hira da ya yi da harshen Hausa da aka sanyawa ido a gidan talabijin da Rediyon kasarnan cewa falsafarsa a fannin mulki ba sata ba ce domin yana sane da cewa za a yi ranar hisabi.
Ji shi:
Na yi farin ciki da mun gina hanyoyi masu inganci waɗanda za su daɗe na tsawon shekaru. Ba irin wadannan hanyoyi da suka yi a baya ba wanda bayan shekaru 2, bayan damina 2 hanyoyin ba za su lalace ba.”
“Har yanzu muna da sauran aiki… shirinmu shi ne, muna son a yi wa duk titunan Kaduna kwalta, duk wanda ya zo Kaduna ba zai ga titin laka ba, duk wani yanki na garin da za ka ziyarta zai samu kwalta da fitilun titinan da ke amfani da hasken rana. Wannan shi ne abin da muka zayyana a ko’ina a Kaduna, a Kafanchan, a Zariya da kuma a dukkan kananan hukumomin kamar Soba, ko’ina. Abin da muke son gani ke nan.”
“Duk da haka, ba za mu iya cimma dukkan tsare-tsaren ci gabanmu ba saboda halin da wannan gwamnati ta hadu da shi. A gaskiya ma mun nemi lamuni don aiwatar da waɗannan ayyukan. “
“Mutane na iya ganin cewa mun aiwatar da wadannan ayyukan da rancen da muka samu. Ba mu ciyo bashin Dubai muka sayi gidaje ko mu je Jabi Road muka gina katafaren gida ba. “
“Ba mu zama kamar irin waɗannan mutane ba. Na zama Gwamnan Jihar Kaduna da gida daya a titin Danja a Unguwan Sarki Kaduna..Na gama mulkina, Alhamdulillah…wato gidana daya tilo. Ba ni da wani gida.Ban gina babban gida ba. Ba ni ma bukata.”
“Ban saci kudin kowa ba, ina kuma kalubalantar wadanda ke mulkin Kaduna da su fito su rantse cewa ‘ba su taba satar kudi ba, su rantse cewa ba su karbi kobo daga jihar Kaduna ba. “
“Wallahi, a shirye nake in rantse. Ina kalubalantar su (Tsoffin Gwamnonin) da su fito, su fuskanci al’ummar Jihar Kaduna su rantse cewa ba su taba sace kudaden jama’a ba.”
“Mun san su, ba ’ya’yan Dantata ba ne ( fitaccen attajirin Kano) ko ’ya’yan Dangote. Mun san su tun lokacin da muke makaranta. A ina suke samun kuɗin gina waɗannan gidaje? Menene sana’arsu?”
El Rufa’i ya ce irin wannan ba falsafar su ba ce a harkokin mulki domin shugabanci amana ce da Allah ya ba mutum kuma wata rana dole ne shugaba ya tsaya a gaban Allah domin ya yi hisabi.