Ban yi nadama kan rusau din da nayi a Kano ba – Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fadawa Sarki Aminu Ado
Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, a ranar Juma’a, ya shaida wa Sarkin Kano kuma shugaban Majalisar Sarakunan Kano, Mai Martaba, Alhaji Aminu Ado Bayero, cewa bai yi da-na-sanin rusa kadarori da gwamnatinsa ta dauka ba a matsayin haramtattu a doka ba.
Ya bukaci Uban Masarautar da ya ci gaba da tallafawa manufofin gwamnatinsa da aka tsara domin kawo ci gaba a jihar tare da raba ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar.
Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a gidan gwamnatin Kano lokacin da mai martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero tare da hakimai da sauran ‘yan majalisar Masarautar suka kai masa ziyarar Sallah, a wani bangare na gudanar da bukukuwan Sallah Eid El Kabir.
Gwamnan wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya dage cewa bai yi nadama ba kan yadda ake ruguzawa tare da kwato dukiyoyin jama’a da “gwamnatin da ta shude ta bada su ba bisa ka’ida ba tare da raba wa masu hannu da shuni.”
“Mai martaba yana da kyau majalisar Masarautar ta lura da cewa mun fara aikin rusau ne domin dawo da kadarorin al’umma da aka mallaka ba bisa ka’ida ba, kuma za mu tabbatar da cewa an dawo da duk irin wadannan kadarorin domin maslahar mutanen Kano.” Ya kara da cewa.
Gwamna Yusuf, ya yabawa Sarkin da ‘yan majalisar Masarautar bisa wannan ziyara da ta kai irinta ta farko tun bayan hawansa mulki yayin da ya kuma zayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin kwanaki 31 da suka gabata a kan karagar mulki.
Ya bayyana nasarorin da ya samu da suka hada da: biyan kudin NECO ga daliban makarantun sakandare 55,000 da ya kai Naira biliyan 1.5; maido da fitilun tituna; da kuma rage matsalar satar waya a cikin birnin Kano.
Sauran nasarorin, a cewar gwamna Yusuf, sun hada da: sake fara tantancewa don bayar da tallafin karatu na kasashen waje ga ’yan asalin Kano masu digiri na farko; gaggawar biyan albashi da fansho; da kwashe dubban sautunan sharar gida a cikin babban birni.
A nasa jawabin, sarki Aminu Ado Bayero ya ce sun kawo ziyarar ne domin taya gwamnan murnar sallar Eid El Kabir.
Ya kuma tabbatar da a shirye yake ya ba da shawarwarin da za su kasance masu muhimmanci da amfani ga ci gaban jihar.
Sarkin mai daraja ta daya ya kuma yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su taimaka wa masu karamin karfi wajen dakile illolin cire tallafin man fetur.