Bana goyon Bayan tsige Buhari Kuma Ina dalili ~Sule lamido
tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce masu kiraye kiraye kan tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari kan gazawar jagorancin sa ba za su samu goyon bayan sa ba.
Lamido, a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan bikin rantsar da zababbun shugabannin PDP da aka zaba kwanan nan a kananan hukumomi 27 (LGAs) na jiharsa ta jigawa
Tsohon gwamnan, wanda yake cewa ba shi da wani abin da ya saba wa shugaban, ya kara da cewa sukar da ya ke ta samo asali ne daga asalin siyasarsa na fadin gaskiya ga wadanda ke kan mulki
Tsohon gwamnan, wanda ya yi magana a kan batutuwan da suka shafi kasa daban-daban, ciki har da burinsa, ya kuma bayyana imanin cewa lokaci bai yi ba yanzu na furta burinsa. Ya kara da cewa abin da PDP ke bukata yanzu shi ne kwanciyar hankali da kuma dunkulewa.