Bana iya bacci Mai Da’di idan na tuna cewa ‘yan Nageriya mutun milyan 84m ne ke fama da talauci ~Shugaba Tinubu.

Shugaban Kasa Bola Tinubu ta Bakin Ministan ku’di kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ya ce shugaban kasa Bola Tinubu bai ji dadin bacci yadda ‘yan Najeriya miliyan 84 ke fama da talauci ba.
Edun ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da shirin Canjin kudi na Renewed Hope Conditional Cash a Fadar Shugaban Kasa.
Ministan ya bayyana cewa, lamarin ya sa kawo karshen talauci ya zama fifiko ga Gwamnati, inda ya ce tallafin kudi Naira 25,000 bisa sharadin mikawa gidaje miliyan 15 zai taimaka wajen magance matsalar ga wadanda suka fi fama da talauci cikin kankanin lokaci.
Gwamnatin ta ce, na tsawon watanni uku, magidanta miliyan 15 a fadin kasar za su samu tallafin kudi na Naira 25,000, wanda kuma aka samar da Naira tiriliyan 1.125 domin hakan.
Yana kaiwa sama da ‘yan Najeriya miliyan 61 masu rauni kuma an tsara shi don rage radadin tallafin man fetur.
An kiyasta yawan al’ummar Najeriya sama da miliyan 225, a cewar Worldometer, wanda ke ba da kididdigan duniya na zahiri.