Bana Iya Zuwa Garinmu Saboda Hare-Haren Boko Haram Na Karuwa, Sunyi Wa Mutane 75 Yankan Rago A Dare Daya Sanata Ndume.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Sanata Ali Ndume dake wakiltar mazabar Borno ta kudu a majalisar tarayya ya bayyana cewa baya iya zuwa garinsa na Gwoza saboda hare-haren Boko Haram na karuwa.
Ya bayyana hakane a wani zaman tattaunawa na masu ruwa da tsaki da aka yi da kwamitin majalisar tarayya dake kula da ayyuka na musamman da hukumar kula da yankin Arewa maso gabas, NEDC a Borno.
Ndume yace sojoji na iya bakin kokarinsu kuma yana jinjina musu amma maganar gaskiya itace abin yayi yawane. Mun ruwaito muku cewa sanata Ndume yace akwai dare 1 da Boko Haram suka fitar da manyan mutane 75 a Gwoza wansa wasu ya sansu, suka kaisu mayankar garin suka musu yankan rago, Yace 2 ne kawai suka tsira saboda suma sun yi kamar sun mutu.
Yace akwai kuma randa suka fitar da matasa suka musu kisan gilla, Ndume yace wannan kadanne daga irin ta’addancin da Boko Haram ke yi. Yace mutane na mutuwa akai-akai kodai saboda yunwa ko kuma saboda harin Boko Haram.
Ya cewa kwamitin da zasu je sansanin ‘yan gudun hijira da sunga irin halin gamayyar mutane ke ciki. Yace shi kanshi a matsayinsa na sanata baya iya zuwa Gwoza, mahaifarsa.