Bani da hannu kan satar bilyan N37bn Kuma ban san barawon ba ~Sadiya farouq
Tsohuwar ministar harkokin jin kai da walwala da ci gaban al’umma, Hajiya Sadiya Farouq, ta musanta cewa akwai alaka da wani Mista James Okwete, wanda hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ke bincike a kan zargin almundahana da kudade.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce tana binciken Okwete kan badakalar Naira biliyan 37.
Farouq, a cikin wata sanarwa da mai taimaka mata kan harkokin yada labarai, Alexander Udeh, ya fitar, ta ce ba ta san Okwete ba, kuma ba ta taba sa ya wakilce ta ba a kowane matsayi.
Sanarwar ta ce: “ Hankalina ya karkata ga yadda wasu kafafen yada labarai na yanar gizo ke wallafawa suna kokarin danganta sunana da ayyukan wani Mista James Okwete, wanda hukumar EFCC ke bincike a kansa kan zargin almundahana da kudade.