Labarai

Bani da wata manufa ga Musilmin Abuja sai Alkhairi ~Cewar Ministan Abuja Wike.

Spread the love

Wike ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin gudanarwa na masallacin kasa na Abuja, karkashin jagorancin shugabanta, Etsu na Nupe, mai martaba, Alhaji Yahaya Abubakar a wata ziyarar ban girma da suka kai masa a ranar Laraba.

Ministan ya karyata rahotannin da ake yadawa cewa gwamnatinsa a Abuja na inganta manufofin da suka sabawa tsarin addinin Musulunci.

Ya ce masu kokarin karfafa ra’ayin addini suna yin hakan ne ta hanyar yaudara domin samun wasu maki na siyasa.

Wike ya lura cewa ba shi da wani dalili na tayar da kalaman kyama ga kowane kungiyoyin addini amma ya goyi bayan duk wanda ke da manufa ta gaskiya.

Ya kuma ba da tabbacin cewa FCT ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tallafa wa kula da Masallacin kasa, ko kuma Cibiyar Ecumenical ta kasa, kasancewar an ayyana shi a matsayin abin tarihi na kasa.

Ministan ya kuma yi kira ga malaman addini da su yi wa’azin hadin kan kasa da zaman lafiya.

Wike ya ce, “Babu wata gwamnati da za ta yi jinkirin tallafa wa ko kiyaye wani abin tunawa na kasa, na Kirista ko Musulmi.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button