Bani Da Wata Matsala Da Dukkan Jaruman Kannywood Inji Anas Ɗan Alhaji.
Ni sabon jarumi ne kuma mai zuba dukiya in ɗauki nauyin shirin Fim a masana’antar shirya fina finan hausa ta kannywood.
Suna na Anas Idris Mustapha amma ana kirana da suna Anas Dan Alhaji, an haifeni a Jihar kaduna Cikin kaduna ta Arewa a cikin Unguwar kawo kaduna, Na fara karatuna na firamare a (Primary Onward Nusary and primary school kawo) Daga nan natafi (Morlat Junior Secondary School Hayin banki kawo), Daga nan na tafi Babban Sakandire a (Kaduna Capital School), bayan na kammala Babban Sakandire ɗina, daga nan na tafi Federal University Gusau na yi karatun share fagen shiga Jami’a Daganan na dawo Makaranar koyon kiwon lafiya ta Maƙarfi (Shehu Idris School of Health tech Makarfi) , inda na karanta fannnin kula da ɗakunan bincike (Technical Labrotary Science) Difiloma (Diploma).
Na fara sha’awar wannan Sana’a tun Lokacin dana kammala Sakandire (Secondary School) ɗina ina nufin wajen shekaru shida kenan a baya Inata ƙoƙarin sanin yadda Sana’ar take kafin in shiga cikinta gadan gadan, domin kada in shiga da jahilcinta saboda kasan Allah ma S.W.A yana cewa ka sanni kafin ka bauta Mani. Kuma duk abinda zakayi arayuwa idan baka san abunba kace zakai mashi karan tsaye to tabbas hanyar bazata bulleba.
Haka yasa na ɗauki lokaci ina bibiyar lamarin daga baya kuma har na tafi karatu domin Komi zakayi arayuwa yanzu ilimi shine jagora, Bayan dawo wa na daga karatu dama akwai abokina ko ince Aminina wanda shi yana cikin masana’antar sosai Amma yaɗan ja baya ne kaɗan saboda wasu harkokin Rayuwa da muka zauna dashi Muka tattauna sai muka ga cewa ya dace mu buɗe wani sabon kamfani Muyi masa Rijista kamar yadda doka ta tanaza. Shine muka zauna muka yanke shawaran sunan kamfanin mu mai suna ONE FAMILY PRODUCTION.
Wannan shine sabon kamfanin mu kuma munyi masa Rijista da hukumar tace Fina Finai ta Jihar kano, yanxu haka kamfanin mu mun shirya manyan Fina Finai Guda hudu biyu suna kasuwa biyu kuma suna Hanya Akwai Raliya akwai jigon Rayuwa akwai Amrah akwai ASHABUL UKDUD, Raliya da Jigon Rayuwa suna suke kasuwa.
Fim ɗin dana fara fitowa a ciki shine jigon Rayuwa wanda nida Salisu S Fulani da momy Gwambe da sauran Ƴan wasa manƴa kusan guda talatin muka fito a film ɗin kuma nine na zuba dukiya na ɗauki Nauyin fim ɗin kuma Alhamdu lillah yanzu haka yana kasuwa kuma ya karbu sosai ga Jama’a, domin kusan kullum waya bata yankewa akan yabo da sharhi akan fim ɗin.
Ina sha’awar naga na zuba dukiya inga ana shirya fina finai da suka shafi Al’adunmu da kuma Addinin mu saboda ni na Fito ne a tsa tson Gidan Malamai Domin zuri’ar Gidanmu sune limamai na Yankin kawo Gaba Daya, dole inyi ƙoƙarin ƙara Ha’b’baka abinda ya shafi Addinin mu da kuma Al’adarmu.
Ina kira ga matasa dasu tashi sukama Sana’a domin kada suce wai dan sunyi karatu Bazasu nemi sana’a ba Ninan kaina koda nake karatu ban tsaya anan ba domin ina aikin printing a Ajams printing press dake nan lokoja road anan kaduna kuma Aikina bai hanani karatu ba kuma bai hana ni sana’a ta Fim ɗina ba saboda haka matasa mu tashi kwarai da gaske mu nemi sana’a domin itace Garkuwan mu.
Bani da wata matsala da dukkan jaruman kannywood da ma’aikata da kowa da kowa muna ganin mutuncin juna kuma muna daraja juna Daidai Gwargwado.
Masoya na ina maku fatan Alkhairi ubangiji Allah ya barmu tare kuma kusani kofata a buɗe take idan akwai shawarwari ko kuma wasu bayanai da suka shafi masana’antar mu, ko kuma kamfanin mu na One Family production ku nemeni ta Kafafen sada zumunta (social media) ta Facebook Hon Anas Idris Mustapha
Instagram Mrz_anas ku neme ni tanan domin mu rinƙa sada zumunta. Masoya kune Farin cikn mu sai da ku zamu iya kaiwa Allah ya shige mana gaba kuma ubangiji Allah ya ba kowa sa’a akan Sana’ar sa ta Alkhairi Amen nagode.