Bani da wata matsala da Tinubu, kawai ina kalubalantar tsarin INEC – Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, LP, Peter Obi, ya ce ba shi da kishi ga zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, game da ayyana shi da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a cikin hirar da aka yi da shi a tashar talabijin ta Arise TV ranar Litinin.
Ya ce: “Ba ni da wata matsala da Tinubu. Shine wanda nake matukar girmama shi a matsayina na dan uwa kuma na dauka a matsayin uba.
“Ina kalubalantar tsarin da INEC ta bayyana shi a matsayin zababben shugaban kasa. Ba ni da wata matsala game da ayyana shi a matsayin zababben shugaban kasa.”
Obi ya roki hukumar zabe da ta tashi tsaye wajen ganin ta taimaka wa Najeriya wajen gina martabar duniya.
“Mun kuduri aniyar samar da sabuwar Najeriya. Dole ne mu yi duk abin da yake daidai.
“Muna buƙatar gina cibiyoyi masu ƙarfi na dimokuradiyya waɗanda za su koya wa mutane abin da aikinsu ke buƙata da kuma abin da gwamnati ke nufi,” in ji shi.