Labarai

Bankin duniya ya Hana Buhari bashin Dola $1.5bn

Spread the love

Rahotanni sun bayyana cewa Bankin Duniya ya hana Najeriya bashin kimanin dala biliyan 1.5 sakamakon faduwar darajar Naira a kasuwar duniya.

Bankin ya bayyana cewa sai Najeriya ta ƙara ƙarfafa matakan farfaɗo da darajar naira kafin ya amince da rancen dala biliyan 1.5 da ƙasar ke buƙata.

Rahoton ya fito ne a ranar Alhamis daga bakin daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Shubham Chaudhuri.

Daraktan ya bayyana hakan yayin da dala ke ci gaba da wahala a kasuwa, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito

A watan da ya gabata an sayar da dala kan kusan naira 500 a kasuwar bayan fage.

Najeriya ta nemi rancen ne domin farfaɗowa daga matsalar tattalin arziki da annobar korona ya haifar da kuma faɗuar farashin ɗanyen mai a kasuwa Sources hausa Post

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button