Labarai

Bankwana da Majalisar ga wasu Ayyukan Sanata Uba sani a Majalisa ta Tara.

Spread the love

A daidai lokacin da ake Shirin kwana da Majalisar dattijai ta Tara ga wasu daga Cikin kudrorin Sanata Uba sani Kuma Zababben gwamnan jihar Kaduna

(1) Kudrin Kwalejin Ilmin dake Giwa, Federal College of Education, Giwa Kaduna State (Est, etc) Bill 2019 (SB. 121). Sanatan ya Samar da Kudrin ne domin kawo karshen matsalar karancin ilimi a yankin na karamar hukumar Giwa.

A ranar 9 ga watan Maris ‘din shekarar  2019 ne manya-manyan masu ruwa da tsaki na karamar hukumar ta Giwa, tare da Sanata Uba Sani, su ka gudanar da taron jin ra’ayoyin jama’a, wanda kwamitin kula da karatun gaba da Sakandire da asusun tallafa ga manyan makarantu TETFund) su ka shirya wanda al’umma tuni sun bayar da goyon baya kuma kawo yanzu kudirin ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar dattijan Nageriya a ranar 15 ga watan Yuli na shekara ta 2020 ne aka karanta shi karo na farko a zauren majalisar wakilai a ranar 3 ga watan Disamba na shekara ta 2020, domin haka yanzu majalisar wakilan Nageriya ake tsumayi ta kammala nazari kafin a mikawa ga shugaban kasa ya sanya hannu.

(2) Kudrin asibitin Rigasa, Federal Medical Center Rigassa, Kaduna State (Est., etc.) Bill 2019 (SB.169) Sanatan yayi yunkurin Samar da wannan asibiti ne Tare da duba da sakamakon yadda Al’ummar ke fama da matsalar karancin cibiyoyin koyon lafiya. Musamman mata masu haihuwa da yara masu fama da cuta kala-kala da sauransu.

A ranar Sha takwas 18 ga watan Fabrairu na shekara ta 2019, masu ruwa da tsaki na Rigasa suka halarci taron jin ra’ayoyin jama’a a kan kudirin, wanda kwamitin Lafiya na majalisar dattijan Nageriya ya shirya.  tuni Kudrin shima ya samu amincewar kwamitin da Kuma jama’ar gari.

tuni dai wannan kudirin ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar Dattijan Nageriya a ranar 3 ga watan Disamba na shekara ta 2020, wanda majalisar Wakilai kawai ake jira, kafin a mika shi ga shugaban kasa ya sanya hannu.

(3) Kudrin gyaran Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kuɗi,  Doka 2020. 

Sai Kudirin Gyaran dokar Bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade ta shekara ta 2004 da Sanatan ya gabatar  a gaban majalisar a shekara ta 2019, da nufin inganta bangaren ajiya da hada-hadar kudaden Nijeriya Wanda yanzu haka tuni shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu wanda ya zama tabbatacciyar dokar tarayyar Nijeriya, a ranar 13 ga watan Nuwamba na shekara ta 2020, wannan sabuwar dokar da aka yi wa kwaskwarima, tuni ta ha’de kafa’da da kafa’da da sauran kasashen duniya, wadda hakan na nufin dokar zata inganta tsarin karba da kuma bada Lasisin gudanar da Bankuna, sannan dokar za ta samar da damar bayyana zahirin haqqi ga babban bankin Nijeriya da sauran cibiyon hada-hadar kudade ta Nageriya.

Haka kuma, dokar za ta sa ido a kan kamfanonin kimiyyar sarrafa kudade, da irin hukuncin da zai biyo bayan a duk wata badakala ga duk harkallar kudi da wasu ke shirya.

(4) Kudrin Kula da Kariyar Dokar Iyayen Yara na 2019 (SB198) Sanata Malam Uba sani ya gabatar da wannan Kudri gaban majalisar dattijan Nageriya ne da nufin bawa yara mahimmanci ta hanyar tsari Mai kyau domin rayuwar su ta gobe mai zuwa.

(5) Kudrin Kwalejin fasahar gandun Daji dake Birnin gwari, Federal College of Forestry, Technology and Research, Birnin Gwari, Kaduna State (Est, etc) Bill 2019 (SB201) 

wannan Kudri na fasahar sanin gandun Daji zai bayar da dama ga matasan Yankin wajen samun Ayyukan yi tare da samun damar cin moriyar da ke tattare da albarkar gandun Dajin. 

(6) Kudrin sauya Kwalejin Fasahar Kaduna zuwa Jami’ar fasaha University of Technology Kaduna (Est, etc) Bill 2019

Samun gyaran wannan jami’a zai karfafawa matasa gwiwa musamman masu baiwar kirkire-kirkiren zamani za’a samu sabbin masana’antu na zamani da dama wanda hakan zai magance matsalar zaman banzan matasa a yankin. Kudrin ya tsallake Karatu na biyu.

(7) Kudrin makarantar Fasahar Sadarwa ta Kaduna ta Kudu (Est., etc.) Bill 2020 (SB.407)

Malam Uba sani ya gabatar da wannan Kudri ne da nufin koyar da fasahar zamani musamman kasuwanci ga matasa hakan na bawa matasa damar shiga sahun manya-manyan masu fasahar sadarwar zamani na duniya.

(8) Kudrin Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya 1999 (Alteration) Bill 2020 (SB. 410)  Sanata Malam Uba sani ya gabatar da Kudirin ga majalisar dattijan Nageriya ne da nufin Samar da dama ga gwamnonin jihohi domin basu ikon zaben alkalai daga hukumomin shari’a na jihohin su, wanda hakan zai bawa Gwamnatin jiha damar aiwatar da Ayyukansu cikin sauki duba da Alkalin ya kasance zabin Gwamnatin jihar musamman wajen gudanar da shari’o’i cikin sauri shi ma wannan Kudri tuni ya tsallake karatu na daya1 a zauren majalisar dattijan Nageriya.

(9) Kudrin Dokar Musanya da sa ‘idon chanji na kasashen waje  (Kwanawa & Kulawa) Dokar 2004 Aiwatar da Bill na  2020 (SB. 525) za’a kawo karshen hau-hawar farashin kayayyakin da ake shigo dasu Nageriya ta barauniyar hanya ta hanyar wannan Gyaran fasali.

(10) Kudrin Dokar Makamai Cap F28 FN (gyara) Bill 2020 (SB. 549) Kudrin Gyaran dokar makamai zai kawo karshen masu mallakar makamai ba bisa ka’ida ba musamman a wañnan Lokaci da ake fama da matsalar ta’addanci a Nageriya musamman arewacin na Nageriya.

Sanata Uba sani ya gabatar da Kudrorin sama da ashirin tsawon zaman sa a majalisar Dattijan Nageriya daga Shekara ta 2019 zuwa yau, haka zalika Sanata Uba sani a halin yanzu shine Dan takara Mafi kwarjini da tarin jama’a mabiya a duk cikin ‘yan takarar Neman zama Gwamnan jihar ta Kaduna Malam Uba sani wanda tuni ya sami Amincewa daga Gwamnan jihar kaduna Malam Nasir Ahmad El Rufa’i yasa alwashin dorawa daga inda Gwamnan ya tsaya a kokarin sa ciyar da Kaduna zuwa mataki na GABA…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button