Labarai

Barawon dollars Bai Isa ya koreni a APC ba sai dai a mutun wallahi ~Inji dan Majalisar APC Tijjani jobe

Spread the love

Rikincin siyasa a Jihar Kano Wani dan Majalisa a Jam’iyar APC Mai wakiltar Dawakin Tofa Rimin Gado da Tofa
Hon ngr Tijjani Abdulkadir Jobe yayi kaca kaca da Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a wani jawabi nasa Dake kunshe a cikin wani bidiyo dayake Taron ganawa da magoya bayansa an jiyo Dan Majalisar wakilai Cikin fushi Yana Cewa mu ba zamu zabi barawo ba Kuma wallahi Babu Wanda ya Isa ya cire ni daga Jam’iyar APC ba dan Sarki ba ba dan Gwamna Babu Wanda ya Isa koshi waye sai dai a mutu ko ai rai Lamarin dayasa mabiyansa Suka Fara Kiran Ganduje da barawon dollars suna masa Ihu,

Wannan Rikincin siyasa Dake tsakanin Ganduje da Dan Majalisar wakilan ya samo asali ne tun Lokacin da aka Fara rade radin Cewa Dan Gwamna Ganduje Eng Umar Abdullahi Ganduje zai tsaya takarar neman kujerar Majalisa Mai wakiltar Dawakin Tofa rimin gado da Tofa wato Mazabar da shi Hon Tijjani jobe ke wakilta.

Rikincin siyasa dai a Jam’iyar APC a jihar Kano wani Abu ne da Jama’a Suka Saba dashi ko kwanakin baya an jiyo dan Majalisar wakilai Mai wakiltar birni da kewa Hon Sha’aban sharada shine Yana Cewa Babu uban da ya Isa ya Kuma duk Wanda ya raga Masa Allah ya tsine Masa albarka.

Jam’iyar dai na fama da rikincin gida a jihar Kano..

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button