Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado Ya shilla kasar Sudan domin magance Matsalar daliban Likitanci ‘yan Asalin Jihar Kano da Suka Makale a can.
Shugaban gudanarwar korafin jama’a da yaki da cin hanci da rashawa (PCACC) ta jihar Kano Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado a farkon wannan makon ya tashi zuwa Khartoum na kasar Sudan domin tabbatar magance Matsalar daliban likitancin da jihar ta dauki nauyi.
Babban mai rike da mukamin shine yake jagorantar ayarin Tawagar jihar kano da suka hada da Babban Mashawarci na Musamman kan Harkokin Ilimi Dakta Hussaini Akilu Jarma, Darektan Gudanarwa da Babban Ofishin Kula da Karatu na Jihar Kano / A.g Kawu Nasiru da sauransu.
Muhuyi Magaji wanda a yanzu haka yake kasar Sudan a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar SAHELIAN TIMES ya ce, “wannan kawai wani mataki ne na magance matsalar wannan daliban da suka makale a wasu kasashe daban daban.
Barista ya Kara da Cewa zan yi iya bakin kokarina Domin ganin ba su sake yin korafi ko kuka ba” In ji shi.
Jaridar ta tattaro cewa fatan dalibin na Matsalar su ya kawo karshe bayan shugaban yaki da rashawa ya sauka a Khartoum.
Wata daliba mai suna Zainab Bala Isah dalibar jami’ar musulinci ta Omdurman a yayin da take nuna godiyarta ta ce sun kasance tare da daukar Tsawon Lokaci suna korafi ba kakkautawa game da matsalolin su na mugun kishin Ruwan bukata a ‘yan shekarun da suka gabata“ amma bayan mun kai kukanmu wurin Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado a cikin kasa da wata guda, yanzu gashi a nan tare da mu yau a Sudan. “
Yayin da take godewa Rimin Gado ta ce, “mun san yadda ofishinku yake da cunkoson aikace aikacen Jama’a amma duk da hakan, ka samu Lokacin halartar matsalarmu.” Inji zainab…
Barista Muhuyi Magaji dai ya shahara wajen sharewa Jama’a kokensu a duk Lokacin da aka Kai korafi Ofishin sa…