Labarai

Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Kai Tiriliyan 31~DMO.

Spread the love

Ma’aikatar dake kula da ciwo bashi na Gwamnatin Tarayya, DMO ta bayyana cewa bashin da ake bin Najeriya yanzu ya kai Naira Tiriliyan 31.

Ya kuma kara da cewa jimullar bashin wanda ake bin Gwamnatin tarayya da jihohi 36 da babban birnin tarayyane suka kai yawan Hakan.

Wannan bayani ya tsayane a ranar 30 ga watan Yuni na 2020. Wanda ya kara nuni da, yawan bashin Najeriyar ya karu da Tiriliyan 2.38 cikin watanni kadan.

Ko a watannan da ya gabata Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Alhaji. Atiku Abubakar yayi kira ga ‘yan Najeiya da kar su amince Shugaba Buhari ya kara ciyo Bashi alhali Babu abinda ake wa kasar da Bashin sai dai Tarin bashin da Gwamnatin APC ke Tarawa Kasar Inji Atiku.

Sai dai Wasu talakawa na Ganin wannan Ikirari na Atiku Siyasace, su basuda damuwa ko bashin nawa gwamnati zata ciyo.

Masu karatu menene Ra’ayinku akan Yawan Bashin da ake bin Kasar Nan…?

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button