Bashin da wasu gwamnoni masu barin gado suka ciyowa jihohin su
A ranar 29 ga watan mayu ne wa’adin wasu gwamnonin Najeriya zai kare, shiyasa mukayi duba akan irin bashin da za su bari a jihohin da suka mulka na tsawon shekarun da sukayi suna mulki. Ga jerin lissafin nan a kasa..
Sokoto
A shekara ta 2015 gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya tarar da bashi N11.66bn, amma kuma a shekara ta
2022 bashin ya karu zuwa N90.59bn
ya canza zuwa +677%.
Katsina
A shekara ta 2015 Gwamnatin Aminu Bello Masari ta iske bashin N11.49bn, amma a shekarar
2022 bashin ya karu zuwa N62.37bn, ya canza zuwa +443%.
Neja
Shima gwamnan jihar Neja mai barin gado a shekarar 2015 ya tarar da bashin N21.50bn, amma kuma bashin ya kara yawa a shekarar 2022 zuwa N95.59bn, ya canza zuwa +345%.
Binuwai
Haka zalika gwamnan jihar Binuwai mai barin ga a shekarar 2015 ya riski bashin N39.94bn, amma kuma bashin ya karu a shekarar 2022 zuwa N141.29bn, ya canza zuwa +254%.
Taraba
A shekarar 2015 gwamna mai barin gado na Taraba ya tarar da bashin N27.65bn, amma a shekarar 2022 bashin ya tashi zuwa N87.96bn, ya canza zuwa +218%.
Abiya
Haka lamarin yake a jihar Abia, inda gwamna mai barin gado a 2015 ya tarar da N33.53bn a matsayin bashi, yayin da bashin ya tashi a 2022 zuwa N103.71bn, ya canza zuwa +209%.
Enugu
A Shekarar 2015 Gwamnatin jihar Enugu mai barin gado ta tarar da bashin N37.55bn, amma a shekarar
2022 bashin ya haura zuwa N91.86bn, ya canza zuwa +145%.
Zamfara
A shekarar 2015 Gwamnatin Zamfara mai barin ga ta iske bashin N46.28bn, amma kuma bashin ya tashi a shekarar 2022 zuwa N112.19bn ya canza zuwa +142%.
Ebonyi
Gwamnatin jihar Ebonyi mai barin gado a shekarar 2015 riski bashin N34.17bn, yayin da bashin ya tashi a shekarar
2022 zuwa N76.49bn, ya canza zuwa +124%.
Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa mai barin gado a 2015 ta tarar da bashin N22.19bn, amma kuma bashin ya karu a shekarar
2022 zuwa N43.95bn ya canza zuwa +98% karuwa
Kano
A shekarar 2015: Gwamnatin jihar Kano mai barin gado ta tarar da bashinN65.01bn, amma kuma bashin ya karu a shekarar 2022 zuwa N122.36bn, ya canza zuwa +88%.
Cross River
A jihar Cross River ma gwamna mai barin gado a 2015 ya gaji bashin N115.52bn, yayin da bashin ya karu a
2022 zuwa N197.21bn, ya canza zuwa +71%.
Kaduna
A shekarar 2015 gwamnan jihar Kaduna mai barin gado ya gaji bashin N49.85bn, yayin da bashin ya karu a shekarar
2022 zuwa N83.29bn, ya canza zuwa +67%.
Rivers
A shekarar 2015 gwamna mai barin gado na jihar Rivers ya tarar da bashin N134.97bn, yayin da bashin ya karu a shekarar
2022 zuwa N225.51bn, ya canza zuwa +67%.
Akwa Ibom
A shekarar 2015 gwamna mai barin gado ya gaji bashin N147.58bn, amma kuma bashin ya karu a shekarar
2022 zuwa N219.27bn, ya canza zuwa +49%.
Delta
A shekara ta 2015 gwamna mai barin gado na jihar Delta ya gani bashin N320.61bn, amma kuma bashin ya ragu a shekarar 2022 zuwa N304.25bn -5% karuwa.
Kebbi
A shekarar 2015 gwamnan jihar Kebbi mai barin gado ya gaji bashin N63.79bn, yayin da bashin ya ragu a shekarar
2022 zuwa N61.31bn, -4% karuwa