Addini

Batanci Ga Annabi: Ka Gaggauta Saka Hannu A Takardar Hukuncin Kisan, Sakon Majalisar Limaman Kano Ga Ganduje.

Spread the love
Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje

Majalisar Limamam Jihar Kano Sun Nemi Ganduje Ya Rattaba Hannun A Kan Takardar Hukuncin Kisan Da Aka Yankewa Matashin Da Yayi Batanci Ga Annabi.

Majalisar Limaman Masallatan Juma’a na jihar Kano ta shawarci gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya sanya hannu a kan tardar Hukuncin kisa da aka yankewa Mawaki Yahya Aminu, wanda ke gabanshi bayan Kotun Shari’ar Musulunci ta zartar da hukuncin.

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano dai ta yanke wa Yahya Aminu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa saboda yin kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (s.a.w).

Haka zalika majalissar ta yaba wa babbar kotun Shari’ah saboda zartar da hukuncin kisa da tayi ga matashin mai shekara 22, Yahaya Aminu.

Shugaban majalisar Muhammad Nasir Adam ya ce hukuncin ya dace kuma bisa koyarwar addinin Musulunci. Ya ce, majalissarmu tana da kwarin gwiwa cewa gwamna Abdullahi Ganduje zai rattaba hannu kan hukuncin kisan. ” Mr. Adam ya gargadi musulmai da su guji goyan bayan duk wani yunkuri na dogaro da sunan annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi.

Hakanan, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Harun Sani Ibn Sina, ya goyi bayan hukuncin Kotun Shari’ar Musulunci wacce ta yanke wa Mista Aminu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa.

Mr. Ibn Sina ya ce Hukumar na da cikakken goyon baya ga hukuncin kamar yadda aka ginata kan tanadin Shari’ah (shari’ar Musulunci).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button