Kasuwanci

Batun Bude Kasuwanni Yau A Kaduna Dai Babu Shi.

Spread the love

Rahotannin dake iskemu daga jihar Kaduna na cewa batun bude Kasuwannin jihar a yau ba zai yiwu ba, saboda ba a kammala feshin maganin kashe kwayoyin cututtuka ba.

Idan baku manta ba a jiya Laraba mun kawo muku rahoton cewa injinan feshin maganin kashe kwayoyin cututtuka wadanda za a feshe Kasuwannin jihar da su sun ki suyi aiki.

Wakilinmu Muktar Onelove Kaduna ya zanta da wani daga cikin masu ruwa da tsaki akan bude Kasuwannin, inda ya shaida masa cewa sai gobe Juma’a za a bude Kasuwannin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button