Ilimi

Batun Bude Makarantu Gwamnan Jahar Jigawa Ya Tattauna Da Ministan Ilimi Adamu Adamu.

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya ziyarci ministan ilimi a ofishan da ke ma’aikatar ilimi ta kasa dake birnin tarayya Abuja.

Gwamnan ya ziyarci ofishin ministan ne da nufin su tattauna bisa yadda za’a bude makarantu domin dalibai su cigaba da gudanar da harkokin karatun su, a yayinda kuma kasar ke yaki da yaduwar annobar covid 19.

Gwamnatin tarayya tuni ta bada umarnin kada a bude makarantu domin a kauracewa karuwar yaduwar annobar a inda kuma a gefe daya aka dakatar da masu kammala karatun sakandire rubuta jarrabawar waec.

Daga Haidar H Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button