Batun Sakin Aure a film Daga Karshe dai Malam yayi amai ya lashe.
Shahararran Malamin Addinin Muslunci Dr Bashir Alfurqam
Yayi amai ya lashe Kan Batun Sakin auren Yan film
Malam Yace Batun Cewa idan mutun ya saki matarsa ta film ya saki matarsa ta gida Dr Bashir yayi Karin haske a Cikin wani gajeran bidiyon inda yake Cewa Maganar tana da tafsiri Magana ce a dunkule Kuma shi Abinda yake nufi shine idan Mata da miji na zahiri sun kansance ‘yan wasan kwaikwayo Kuma aka sakasu a film daya Acikin Shirin film din Kuma mijin ya furta Cewa ya saki matarsa a a film din to a zahiri aurensa na Gaskiya tsakaninsa da ita ya mutu ba auren film ba.
Malam Yace Amma idan Daman can ba ma’aurata bane idan ya saketa to a zahiri aurensa nanan Inji malamin.
Dukda a baya malamin Cewa yayi idan mutun ya saki matarsa ta film matarsa ta Zahiri ta saku baiyi Karin bayani ba…
Jama’a da dama sunyi CeCe kuce Kan Wagga fatwa..