Labarai

Batun Wawushe 774 Na Dibar Sabbin Ma’aikata: Minista Festus Keyamo Ya Caccaki ‘yan Majalisa.

Spread the love

Festus Keyamo, Ministan Kwadago da Aiki, ya caccaki ‘yan majalisar a zauren majalisar Kan Batun su na neman karin wasu gurabe na shirin Na Musamman na Gwamnatin Najeriya.

Inda ‘yan Majalisar suka bukaci kashi 30 daga cikin 1000 daga kowace karamar hukuma da Suke wakilta kowane dan majalisar, marasa rinjaye a majalissar sun yi watsi da rukunin wuraren.


Martanin da ya mayar wa ‘yan majalisar, Keyamo . Ya ce mazabun yan majalisun za su amfana da ayyukan na musamman, ya kara da cewa barazanar da ‘yan majalisar ke yi na kin amincewa da jadawalin da aka basu ba lallai bane.

Ya ce wannan dama ba abune da ya shafi hakki ko cancanta ba, a.a wata dama ce kawai da aka basu don ba da shawarar mutane a cikin mazabunsu.

Misali ace za a zaɓi mutum 1000 daga kowace karamar hukuma. Wannan na nufin ko sun ƙi ko sun yarda ba su da mahimmanci saboda mazabunsu zasu kasance suna da cikakkiyar damar Samun 1000 a kowace karamar hukuma.


“Saidai idan suna so su fadawa ‘yan Najeriya cewa sashin wadannan kananan hukumomin ne kawai suke wakilta kuma ba dukkan mutanen karamar hukumar bane.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button