Baya ga umarnin Ganduje, kotu ta sake garkame masallatan Sheikh Abduljabbar da Cibiyoyin addininsa..
Kotu ta Rufe Cibiyoyin Addinin Sheik Abduljabbar.
Gwamnatin jihar Kano ta samu umarnin kotu na rufe Masallacin Sheik Abduljabar da duk wasu cibiyoyin addini mallakin sa tare da hana shi ci gaba da wa’azi a jihar.
Umurnin ya kuma umarci dukkan jami’an tsaro da su kama tare da yanke hukunci a kan duk wanda ya yi kokarin yin biris da umarnin.
Umarnin kotun wanda ya samu daga Ofishin Babban Mai Shari’a na Jiha, Barista MA Lawan, an yi shi ne a Kotun Majistare mai daraja ta daya 12 Gidan Murtala Kano, wanda Mohammed Jibrin ke shugabanta.
Babban alkalin kotun ya bayar da umarnin ne bayan ya saurari takaddar da aka gabatar wa Wada A Wada (PSC) daga ofishin Babban Lauyan Jihar Kano, inda ya nemi umarnin kotun sa da ta rufe Masallacin Sheik Abduljabar da duk sauran Cibiyoyin addini, da kuma dakatar dashi daga cigaba da wa’azi.
Umurnin ya kuma umarci ‘yan sanda, DSS da sauran jami’an tsaro da su tabbatar da bin umarnin tare da umartar su da hukunta duk wanda ya yi kokarin yin hakan.