Bayan anyiwa Shugaba Buhari Allurar rigakafin CoronaVirus Haryanzu Babu abinda ya faru dashi ~Inji Garba Shehu.
Mai Magana da yawun Shugaban Kasa Kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu Yace Dangane da tambayoyin manema labarai suke min a yau, Ina so in tabbatar wa dukkan ‘yan ƙasa, da kuma kawar da kokwanto da rashi fahimta game da lafiyar allurar rigakafin da aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, SAN a safiyar yau.
Bayan ya karbi Allurar yau, Shugaban ya sami nutsuwa kuma ya ci gaba da aikin sa. Idan akwai wasu illoli da suka biyo baya, zai kasance kofarmu a buɗe game da hakan amma har yanzu babu wani abu na illa, mai tsanani ko taushi ga Shugaban. Yana ci gaba kamar yadda ya saba.
Muna fatan wannan zai taimaka wajen isar da sako mai karfi a tsakanin mutane, musamman wadanda ke kokawa game da inganci da amincin allurar.
Garba Shehu
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa
(Kafofin watsa labarai & Jama’a)
Maris 6, 2021