Labarai

Bayan ayyana Ilmin gaba da Sakandire kyauta Gwamna Kefas na Tara ya amince da biyan ‘yan bautar Kasa dubu N50,000 amatsayin alawus-alawus.

Spread the love

Bayan ayyana makarantun gaba da sakandire kyauta da gwamnatin jihar Taraba ta yi, gwamnan jihar, Dr Agbu Kefas ya amince da biyan kudi naira 50,000 a matsayin alawus na lafiya ga masu yi wa kasa hidima, NYSC da mambobin kungiyar zuwa makarantu.

Ya kuma ce za a ba su karin alawus na Naira 10,000 duk wata a matsayin tallafi daga gwamnatin jihar.

Kwamishiniyar Yada Labarai ta Jihar, Zainab Usman Jalingo, a cikin wata sanarwa a yau ranar Lahadin ce wacce ta sanar da sabbin matakan, ta sanar da cewa, gwamnatin Kefas ta kuma ware Naira 25,000 a matsayin alawus alawus na kowane wa’adi ga mambobin kungiyar.

A cewarta, “Yawancin sabbin rajista da aka samu a makarantunmu na firamare da sakandare a cikin kwanaki goma da suka gabata ya sa a dauki matakin gaggawa.

“A matsayin agajin gaggawa kan lamarin ilimi, Gwamnan ya amince da wasu makudan kudaden alawus-alawus ga masu yi wa kasa hidima (NYSC) da ke aiki a makarantun jihar Taraba, wadanda suka hada da; Za a kara musu karin naira dubu goma a alawus dinsu na wata-wata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button