Bayan gwamna Umahi, karin wasu gwamnonin adawa 9 za su koma APC, in ji Gwamna Yahaya Bello.
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi ikirarin cewa wasu Gwamnoni tara masu adawa za su tsallaka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Bello ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin da yake bayyana a shirin Siyasar Yau na Channels Television.
A cewarsa, ya yi hasashen gwamnoni 10 za su shiga jam’iyya mai mulki kuma Gwamnan jihar Ebonyi shi ne na farko a cikinsu.
“Na ce akwai gwamnoni 10 daga jam’iyyun adawa da za su koma APC.
“Mun ga guda daya. Wanda yake daidai da goma; Ya shiga cikin mu. Tara saura, “inji Bello.
A safiyar yau, gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), sun sake nanata sadaukarwa da biyayya ga jam’iyyar.
Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal, ya ce: “Dukkanmu 15 muna nan.
“A daidaikunmu mun himmatu ga kyakkyawan shugabanci a jihohinmu daban-daban domin karfafa jam’iyyarmu.