Fashion

Bayan kwanaki kaɗan da aurar da ɗiyarta Gumsu Abacha ga gwamnan Yobe Mai Mala Buni a wani biki da ba a yi wani shagali ba, Matar tsohon shugaban kasa Hajiya Maryam Sani Abacha ta shiga wani babban shagali na cikarta shekaru 73 a duniya.

Spread the love

Wannan lokaci ne na shagalin murna ga dukkan iyalan Gidan, bayan a makon da ya gabata an ɗaura auren Gumsu Abacha a Gidan wanta Muhammad Abacha da ke Abuja.

Hajiya Maryam Abacha ta kasance mace mai kamar maza sakamakon jajircewa wajen kula da yaranta da tayi tun bayan rasuwar Mijinta Janar Sani Abacha shekaru masu yawa.

Allah ya albarkaci Maryam Abacha da ‘ya’ya 10, 3 Mata, Maza 7. Ita ce shugabar Matan Najeriya wato (First Lady) tun daga shekarar 1993 har zuwa 1998 lokacin da Mijin ta ya rasu.

Allah yajiƙan tsohon shugaban kasar Najeriya Janar Sani Abacha Amin.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button