Labarai
Bayan kwashe shekaru Ashirin da biyar a kan mulki Putin ya sake lashe zaben Shugaban Kasar rasha
Vladimir Putin ya godewa ‘yan kasar ta Rasha bayan da sakamakon zaben farko ya nuna cewa ya lashe zaben shugabancin kasarsa da gagarumin rinjaye.
A jawabinsa na nasara, wanda ya gabatar bayan sakamakon ya nuna cewa ya yi nasara da kashi 87% na kuri’un da aka kada, Putin ya kira nasarar da ya samu a matsayin misali na amincewar ‘yan kasar Rasha.
Daga cikin ayyukan da ya ce gwamnatinsa za ta aiwatar a wa’adi mai zuwa akwai karfafa karfin tsaron Tarayyar Rasha da kuma batutuwan ayyuka na musamman. Ya ci gaba da jawabinsa inda ya kira sakamakon zaben a matsayin abin dogaro ga ‘yan kasa.