Bayan na mika Mulki Zan koma daura idan Kuma suka dameni da hayaniya zan tsallake na koma zuwa kasar Niger da zama ~Cewar Shugaba Buhari.
Kalaman na shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa “ba zai yi Kasa a gwiwa ba wajen komawa gida Daura ba bayan ya sauka a mulki” kuma “idan suka yi hayaniya suka dame ni a Daura, zan tafi Jamhuriyar Nijar” kalaman ya harzuka ‘yan Najeriya.
Mutane da yawa sun yi la’akari da cewa sharhin ya kasance mai daukar hankali game da yadda ya yi watsi da kyakkyawar fata da ya samu daga ‘yan Najeriya.
Shugaban ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da wasu manyan baki suka kai masa ziyarar Sallah a fadar gwamnati.
Da dama dai sun fassara kalaman nasa da cewa ba ya sha’awar yanayin rashin tsaro, koma bayan tattalin arziki, da cin hanci da rashawa da ya bar kasar a ciki.
Daga cikin wadanda suka nuna rashin jin dadinsu akwai tsohon babban Limamin Masallacin Quarters na majalisar dokokin kasar, Sheikh Nuru Khalid; dan gwagwarmaya kuma dan jarida, Omoyole Sowore, da wani dan fafutuka, Deji Adeyanju.
Shiekh Khalid ya ce wa Vanguard: “Maganar shugaban kasa abin takaici ne kuma abin ban haushi ne.
“Yana aika da sakon cewa da gangan bai ne nuna isashen sha’awar magance matsalolin da kasar ke fuskanta ba.
“Abin takaici ne yadda shugaban kasa ya fi damuwa da jin dadinsa fiye da jin dadin al’ummar Najeriya. Ya nunawa ‘yan Nijeriya cewa yana da ‘Plan B’ irin nasa.
“Daya daga cikin masu taimaka masa kan harkokin yada labarai ya yi yunkurin kare shi inda ya ce shugaban kasa yana yo da wasa ne kawai. Ba za ku yi wasa da ’yan ƙasarku irin wannan ba. ”
Har ila yau, Sowore, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress, AAC, ya ce babu wata maboya ga Buhari.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari kayi hakuri babu inda zaka buya ga miyagu. Dole ne ku biya bashin da kuka aikata na cin zarafin bil’adama.
“Har ƙarshen zamani, zaluntar ku za ta fisshe ku. Komai tsawon lokacin da za a ɗauka, ba zai damu ba inda kuka ɓuya, za ku amsa laifinku.”