Bayan Rushe Hukumar SARS Shugaba Buhari Zai Rushe Hukumar EFCC Da ICPC.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala shirin Sa Na ruguje hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da takwararta ta ICPC.
Shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan ya karanto wasikar da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya aikawa da majalisar wacce ke dauke da kudirin Na rushe hukumomin guda biyu.
Shugaban kasar yace sabuwar hukumar da za a kafa wacce zata maye gurbin hukumomin EFCC da ICPC din itace zata tabbatar da cewa yan Najeriya sun anfama da kudaden da ake kwatowa daga hannun mahandama barayin gwamnati.
Sedai daga gefe guda wasu masana akan gudanar da harkokin mulki sunyi fashin cewa wannan rushe rushe da canje canje da shugaban kasar yakeyi ba shine mafita ba, wannan alama CE dake nuna rashin iya tafiyar da harkokin mulki.
Menene ra’ayinku..?
Daga Kabiru Ado Muhd