Labarai

Bayan Shafe Sama Da Mako Daya Buhari Ya Bayyana Kaɗuwarshi Game Da Ambaliyar Ruwa A Jahar Kebbi.

Spread the love

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kaɗuwarsa game da ambaliyar ruwan da ta faru a Jihar Kebbi da ke arewacin ƙasarnan, yana mai cewa “ta kawo wa yunƙurimmu na bunƙasa noman shinkafa cikas.

Shugaban ya bayyana hakan ne cikin wani saƙon Twitter da ya wallafa yau Lahadi fiye da mako guda bayan faruwar bala’in, wanda ya yi sanadiyyar lalata gonaki da dama da jawo asarar rayuka.

Ƙananan hukumomin da ambaliyar ta fi shafa su ne Suru Bunza da kalgo da Birnin Kebbi.

Wannan labari maras daɗin ji ya zo a lokacin da manoman Najeriya ke cikin wani hali kuma suke ƙoƙarin girbar amfanin gona mai yawa a wannan shekara domin rage hauhawar farashin kayan abinci.

Daga Amir Sufi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button