Bayyana kadarorin Bogi magu Ya gurfana a gaban Kotun da’ar Ma’aikata.
Mukaddashin shugaban hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu da aka dakatar ya gabatar da kansa a gaban Code of Conduct Bureau (CCB) a Abuja.
Ku tuna cewa CCB ta gayyaci Magu ne bisa zargin rashin bayyana wasu kadarorin sa.
CCB ta nemi Magu a wata wasika mai kwanan wata 2 ga Nuwamba, 2020 don ya zo tare da takaddun shaida na gaskiya (CTC) da Takardar shaidar dukkan dukiyar da ka bayyana ga Code of Conduct Bureau tun da ka shiga aikin gwamnati. Kofe na wasiƙar alƙawarinka, karɓar ka, bayanan ayyukanka da kuma takardar biyan kuɗi daga Janairu zuwa Mayu 2020.
Magu ta bakin lauyan sa, Wahab Shittu, ya nemi CCB da ta kara masa lokaci domin bashi damar samun damar shiga da takardun da suka dace kamar yadda ake bukata.
A cewar rahoton TheCable, shugaban EFCC da aka dakatar ya kasance a ofishin CCB da ke Abuja a ranar Alhamis.
Jaridar TheCable ta kuma ruwaito cewa Magu bai samu halarta ba kasancewar CCB y
Tana yin laccar ta shekara-shekara tare da taken.Mukaddashin shugaban hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu da aka dakatar ya gabatar da kansa a gaban Code of Conduct Bureau (CCB) a Abuja.