Za a cigaba da haska shirin Kwana Casa'in kamar yadda aka Saba - Arewa24 Gidan talabijin na Arewa24 ya bayyana cewar zai cigaba da haska shirin nan nasu na Kwana Casa'in kamar yadda suka saba. Wannan na zuwa ne bayan da hukumar tace finafinai da dab'i ta jihar Kano ta nemi da a dakatar da haska shirin. Shugaban hukumar Afakallahu, ya nemi a dakatar da haska shirin sabida yana ganin akwai abubuwan da suka sabawa al'adu na al'ummar jihar Kano. Sai dai kuma, hukumar gidan talabijin din sun bayyana cewar hukumar ba tada hurumi akan abinda ya shafi gidan talabijin din domin Hukumar NBS ke Alhakin Hakan bawai Wata Jihar ba.. Haka kuma, Gidan talabijin din ya shaidawa manema labarai cewar, basu sabawa dokokin Najeriya ba a nuna shirida suke, dan haka zasu cigaba da nuna shi kamar yadda suka Saba.