Labarai

Bazan daina tattaunawa da ƴan bindiga domin neman sasanci ba – Gwamnan Zamfara

Spread the love

Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ce bazai daina tattaunawa da ‘yan ta’adda ba don ta haka ne kadai za a samu zaman lafiya.

Ya fadi hakan ne bayan an samu nasarar ceto yara 26 ‘yan asalin jihar Katsina, wadanda masu garkuwa da mutane suka kai su jihar Zamfara.

Gwamnan ya tabbatar da an duba lafiyar yaran, an basu sutturu sannan an mayar da su gidajensu, ta hannun kwamishinan jihar, Abubakar Dauran.

Yace tattaunawar tana da matukar muhimmanci don neman zaman lafiya a jihar, Vanguard ta ruwaito.

Gwamnan ya sanar da hakan a wata takarda da Zailani Bappa, mai bashi shawara na musamman a harkar labarai, inda yace sun samu nasarar ceto mutane 26 daga jihar Katsina masu shekaru 8 zuwa 12 daga hannun ‘yan ta’adda ba tare da biyan ko sisi ba.

Kamar yadda takardar ta bayyana, yara matan da aka yi garkuwa da su, ‘yan karamar hukumar Faskari ne da ke jihar Katsina, wadanda ‘yan bindigan suka kai su Zamfara.

A cewarsu, gwamnatin jihar ta gano inda suke kuma Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Alhaji Abubakar Dauran ya tattauna dasu kafin su saki yaran.

“Lokaci bayan lokaci, Dauran yana kokarin tattaunawa da su a maimakon gwamnan don kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar,” a cewarsu.

Yayin da aka amshi yaran , Gwamna Matawalle ya ce mulkinsa ba zai zura ido ya bar tattauanawa da su ba, saboda harbi da yakin ‘yan ta’adda ba zai magance matsalar ba. Daga El-farouq jakada

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button