Bazan Kori shugabanin Jami’an tsaro ba domin na aminta na Kuma gamsu dasu~ Buhari
Babban hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya ce har yanzu shugaban Buhari bazai kori shugabannin ma’aikatar tsaron ba, saboda ya gamsu da aikin su.
Shehu ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayyani a gidan talabijin na Arise TV a daren Litinin.
Ya yi fatali da kiraye-kirayen da ake yiwa shugabannin hafsoshin da za a kora, yana mai bayyana su amatsayin wa’yanda Suka cancanta
An sake samun sabon Batu na neman Buhari ya kori shugabannin tsaro, biyo bayan fille kan akalla manoman shinkafa 43 a Zabarmari da ke cikin Karamar Hukumar Jere ta Jihar Borno a ranar Asabar da ta gabata.
Amma Shehu ya nace kan shawarar korar ko rike wani daga cikin shugabannin hafsoshin gaba daya na Buhari ne.
“Ba ni da masaniya cewa wa’adin shugabannin hafsoshin sojan yana karkashin duk wata dokar ka’ida da ta bayyana karara. Suna aiki ne da yardar shugaban kasa kuma idan shugaban ya gamsu da aikinsu, yana kiyaye su. ya tsaya a teburinsa – tare da girmama yadda ‘yan Najeriya ke ji.
“Ihun da ake yi na ganin an kori Jami’an bai dace ba idan aka yi la’akari da cewa shugaban kasa ba ya karkashin ra’ayin jam’iyyar adawa wacce ta kan yi ta yin hakan a koyaushe. Gabaɗaya ƙaddarar kansa ce; ya yanke shawarar wanda yake rike da shi a matsayinsa na shugabannin rundunarsa da kuma tsawon lokacin da zai yi, ”in ji Shehu