Bazan saka Baki a rikin Rarara Kan saka matar aure a wakarsa ba~ Afakalla
SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya bayyana abin da ya sa ba zai sa baki cikin batun zargin sa ake wa fitaccen mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) da saka wata matar aure cikin bidiyon waƙar sa mai taken ‘Jaha Ta Ce’. Afakallah ya yi magana ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ofishin sa a yau Juma’a. Ita dai waƙar ta Rarara, an tsara ta ne don a nuna alhini kan tashin-tashinar rashin tsaro da ke garuwa a Jihar Katsina, kuma Ali Nuhu da Isa Alolo ne su ka bayar da umarni a wajen shirya bidiyon ta.
To sai dai a cikin wannan makon aka gano cewa ashe jarumar da Rarara ya saka a bidiyoin waƙar matar aure ce, kuma tuni mijin ta ya sha alwashin maka mawaƙin a kotu don a bi masa haƙƙin sa. Mijin, mai suna Abdulƙadir Inuwa, ya shaida cewa auren su da Maryam dududu bai wuce watanni biyar ba, kuma ya sha alwashin maka Rarara a kotu domin ya saka matar sa a fim ba tare da izinin sa ba. Tuni mijin jarumar ya garzaya Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama don a bi masa haƙƙin sa. Da ma dai tun tuni akwai ƙa’idoji da hukuma ta gindaya ga kowanne darakta game da matan da su ka cancanta a saka su cikin kowanne irin shiri don magance faruwar matsala irin wannan. A hirar sa da ‘yan jarida a yau, Afakallah ya ce hukumar sa ba ta samu wani ƙorafi a kan batun na Rarara ba, kuma ba wani jami’i ko wata ƙungiya ko wani abu da aka kawo masu.
“Kamar yadda kowa ya gani a kafar sada zumunta, mu ma haka mu ka gani,” inji shi. Ya ƙara da cewa, “Sannan abin da bai zo gaban ka ba kun ga ai ba za mu ce komai ba har sai mun ga abin da ya bijiro ko kuma aka zo da shi.” A kan batun da wasu ke yi na cewa ko da an kai wa hukumar maganar gaban ta ba abin da zai faru saboda kusancin Rarara da Afakallah, sai shugaban ya yi dariya ya ce, “Ai kun san mutane kowa na da abin da ya ke cewa, ba kuma yadda za a yi ka hana mutum faɗar ra’ayin sa. “Abin da babu shi ba a da tabbacin sa, sai idan har abin ya tabbata, don haka tun kafin a je ko’ina mutane sun ci Talata sun ci larabar abin, sun yi wa kan su hukunci. Don haka yanzu ba za mu ce a’a ko e ba a kan wannan zargi. “Don haka sai abin da ya bijiro za mu tabbatar da yiwuwar sa ko rashin yiwuwar sa.” Film Magazine