Rahotanni
Bidiyon Fatima Ali Nuhu yaja Mata CeCe kucen.
Fatima Ali Nuhu Diya ce ga Shahararran Jarumin Fina finan hausa Ali Nuhu Kuma Fatima itama jaruma ce kwanakin baya da Suka wuce Jaruma Fatima Ali ta wallafa wasu bidiyo a shafinta na Instagram bidiyon da yajawo CeCe kucen daga mabiyanta na shafin Nata Mai dauke da mabiya sama mutun dubu ashirin da Daya 21k+ an hango jarumar tana cashewa da rawa tare da wakokin turanci Wanda wasu ke ganin Hakan yaci Karo da tarbiyar musilmi Dan Arewacin Nageriya.
A Cikin masu mata sharshi wasu na cewa ai Fatima bata gani a Kasa ba ma’ana dai suna jefa Mata habaici cewa barewa bazatayi gudu ‘danta yayi rarrafe ba wasu kuwa bidiyon birgesu yayi inda Suka rinka latsa Mata alamar tambarin soyayya na manhajar Instagram…
To sai muce Allah ya kyauta…