Labarai

Bikin kirsimeti bana buƙatar kowa ya kawomin ziyara ~Buhari

Spread the love

Dangane da yarjejeniya mai karfi da rundunar tsaro ta shugaban kasa ta kafa a kan COVID-19, na takaita manyan taruka, Shugaba Muhammadu Buhari ba zai karbi bakuncin bikin Kirismeti da shugabannin addinai da shugabannin al’umma suka saba yi a Babban Birnin Tarayya ba.

Shugaban kasar ya bukaci dukkan ‘yan kasa da su yi aiki daidai da yadda dokar ta tanada, su kiyaye nisantar jama’a, amfani da abin rufe fuska, yawan wanke hannu da kuma kaucewa cunkoson wuraren jama’a, kasuwanni, cibiyoyin kasuwanci, ofisoshi da wuraren ibada.

Shugaba Buhari ya yi kira ga ‘yan kasar da su rage duk wasu tafiye-tafiye marasa mahimmanci a lokacin hutun.

Yana yi wa kowa barka da Kirsimeti da sabuwar shekara mai zuwa a gaba.

Garba Shehu
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa
(Kafofin watsa labarai & Jama’a)
Disamba 24, 2020

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button