Labarai

Bill Gates da Dangote Sun Yabawa Tinubu Kan Cire Tallafin Man Fetur

Spread the love

Abin da ake sa rai shi ne cire tallafin man fetur zai bude wa Najeriya ingantacciyar damar kudi, in ji Dangote.

Attajirin ‘Dan kasuwan Najeriya, Aliko Dangote da kuma shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates, Bill Gates sun taya shugaba Bola Tinubu murnar cire tallafin man fetur da sauran ci gaba da sabuwar gwamnati ta samu.

Dangote ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a fadar gwamnatin bayan sun gana da shugaban kasar a ofishin sa a ranar Litinin.

A cewar dan kasuwar, abin da ake sa rai shi ne cire tallafin man fetur zai bude wa kasar nan damar zuba jari a wasu fannoni kamar ilimi da kuma ci gaba a tsakanin ‘yan kasa.

Attajirin dan kasuwar ya ci gaba da cewa ziyarar ta ban girma da kuma wata dama ce ta yi wa shugaban kasa bayanin ayyukan gidauniyar Bill Gates da Aliko Dangote, yayin da suke neman karin alkawura daga shugaban kasa, musamman wajen ciyar da bangaren lafiya gaba.

Ya kuma kara da cewa, “’yan Najeriya suna samun abubuwa da yawa don haka ya kamata su kara sa rai. Komai yana da kyau, abubuwa suna tafiya daidai. “

A nasa bangaren, shugaban kasar ya yi alkawarin ba da fifiko kan kiwon lafiya da tsaron ‘yan Najeriya, inda ya jaddada cewa lafiyar ‘yan kasa, musamman ma’aikata na da matukar muhimmanci ga kowace kasa ta ci gaba.

Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ake bukata don ganin ayyukansu a Najeriya da Afirka sun yi nasara, musamman a fannin kawar da cutar shan inna, kyanda, zazzabin cizon sauro da sauran cututtuka a nahiyar.

A cewar shugaban, Gates “yana da duk abin da ake bukata don taimakawa kasashe masu tasowa da yawa”.

Bayan rantsar da shi, Tinubu ya ci gaba da karbar bakuncin manyan baki a Aso Rock.

A safiyar yau ya gana da shugaban Bhanti Artel Worldwide, Sunil Mittal; wanda ya zo tare da Babban Jami’in Kamfanin Airtel Nigeria, Segun Ogunsanya, da sauran mambobin hukumar kamfanin.

Tinubu ya kuma yi wata ganawa da Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Ofishin Albarkatun Makamashi, Geoffrey Praytt, da kuma Babban Daraktan Rukunin Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) Limited, Mele Kyari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button