Bincike: Sheikh Dahiru Bauchi shi ka dai ne mai irin wannan baiwa a duk duniya.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi Shehun darikar tijjaniyya a Nageriya Yana da Baiwa Kamar haka
●Yaransa 95
●Jikoki 406
●Jikokin yaransa 100
●’Ya’ya da jikokinsa duka sunyi karatun addini da na zamani..
● ‘Ya’yansa 77 cikin 95 mahaddata Qur’ani
●Jikokinsa 199 cikin 406 Mahaddata Qur’ani
● Jikokin ‘ya’yansa 12 Mahaddata Qur’ani
●’ya’yansa da jikokinsa da jikokin ‘ya’yansa su 300 kenan mahaddata Qur’ani cikin 601″
● Da Wannan Sheikh ya zamo ďaya tilo tal a tarihin duniya da Allah ya masa wannan baiwa..
Da hakane Cholan Book Of World Records Ta Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi Da Kambun Girmamawa, Sannan Ta Shigar Da Shi Tarihi shine ďaya Tilo A Duniya Da Aka Taba Samun Wannan Baiwa Na Ban Al’ajabi a Tare Da shi….
Allah ya karawa rayuwa albarka Maulana lafiya da jinkiri mai amfani albarkacin Annabi SallalLahu ALaihi WasalLam..