Tsaro

Binciken Kwa-kwaf Yakamata Ayiwa Hukumar Sojan Najeriya Ba Wai Kullum Ayita Kiransu Ana Ganawa Dasu Ba ____Inji Manjo Hamza Almustafa.

Spread the love

Dogarin tsohon shugaban kasar Nigeria marigayi janar Sani Abacha, Manjo hamza Almustafa yace wasu daga cikin manyan sojojin Najeriya ne babbar matsala ga ta azzar rashin tsaron da Najeriya ke fama dashi.

Manjo Hamza ya ce ba tun yau ba suke mita akan hakan amma anki tsayawa abawa batun mahimmanci.

Ya kara da cewa matukar ba a yiwa hukumar sojan Najeriya duba Na tsanaki ba to ko sau nawa shugaba Buhari zai gana da hafsoshin tsaron Najeriya babu abin da zai canza.

Binciken kwakwaf hukumar sojan Najeriya ke bukata ba wai kullum ayita kiransu ana ganawa dasu ba ____inji manjo hamza Almustafa

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button