BINCIKEN KWAKWAF AA Rano Foundation..
Me Kukeson Sani Game Damu?
An Kafa Gidauniyar Tallafawa Mabukata Ta AA Rano Foundation Ne, Domin Taimakawa a ko wane fanni na rayuwar marasa karfi musamman Marasa Lafiya Wadanda Basu Da Kudin Zuwa Asibiti, Da Kuma Tallafawa Wajen Bunkasa Ilimi da Ruwan sha mai tsafta.
Gidauniyar Wadda Take Karkashin Kulawar Alh. Auwalu Abdullahi Rano Shugaban AA Rano Nigeria Limited Tana Ware Miliyoyin Nairori Duk Domin Taimakawa Marasa Lafiya Wadanda Basu Da Galihu. Gidauniya A.A Rano Foundation Bata Bawa Mara Lafiya Kudi A Hannunsa Saboda Gudun Matsala, Sai Dai Takaishi Asibiti Ta Kuma Biya Masa Kudin Magunguna Ko Kudin Aiki Har Zuwa Lokacin Da Zai Warke.
A.A Rano Foundation Tana da Wakilai a Asibitin Nassarawa Dake Garin Kano Da Kuma Asibitin Malam Aminu Kano Duka Dai A Kano. Mara Lafiyar Zai Iya Zuwa Daya Daga Cikin Asibitocin Kaitsaye Ya Nemi Wakilan A.A Rano Foundation.
Hauwa Adamu itace mai magana da yawan Gidauniyar, Kuma ta Nuna Takaicinta Akan Yadda Talakawa Suketa Bulayi Wajen Neman Kudin Magani. Wani Mara Lafiyar Ma Za Kaga Kudin Da Ake Nema Basu Wuce Dubu Biyar Ko Goma Zuwa Ashirin Ba, Amma Sai Kaga Sanadiyyar Rashin Samun Wannan Kudin Ya Galabaita, Wani Ma Sai A Rrasa Ransa Saboda ‘Yan Kudi Kalilan.
Insha Allahu Gidauniyar Tallafawa Mabukata Ta A.A Rano Foundation Zata Share Muku Hawaye.
Wannan Sakon kar ta kwana ne domin wayar da kan Al’uma a kan Gidauniyar Tallafawa Mabukata Ta AA Rano Foundation.