Birtaniya ta kama wani mutum saboda ƴaɗa bidiyon shekau ta kafar sada zumuntar WhatsApp
An tsare wani ɗan shekara 43 a Birtaniya a ranar Alhamis kan zargin rarraba bidiyon shugaban ƙungiyar Boko Haram ta kafar WhatsApp.
Shakil Chapra, daga yammacin London, ana zarginsa da laifin yaɗa ayyukan ta’addanci wanda ya saɓa wa dokar ta’addanci ta 2006.
An shaida wa Kotun majistire a tsakiyar London cewa ya yaɗa bidiyon ne a ranar 11 ga Satumban bara.
Ba a shigar da wani koke ba, amma Chapra ya yi magana ne kawai don tabbatar da sunansa da ranar haihuwa da kuma adireshinsa a zaman kotun na ɗan lokaci.
Kotun ta buƙaci ya sake bayyana gaban kotun sauraren ƙararrin laifuka a ranar 20 ga Nuwamba.
A watan Yulin 2013, gwamnatin Birtaniya ta saka Boko Haram da ke ta’ddanci a Najeriya a matsayin ƙungiyar ƴan ta’adda. Daga Comr Zakari Ya’u Salisu, Gombe