Labarai

Biyan Bashin Buhari: Mugun mutum ne kawai yake kasa biyan bashin da ake binsa – Fadar Shugaban Kasa

Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya bayyana dalilin da ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yin nade-naden mukamai a minti na karshe da kuma neman amincewar kashe kudade.

A ranar Laraba, Buhari ya bukaci majalisar dattawa da ta amince da bukatar biyan wasu makudan kudade a matsayin basussuka.

Kudaden da suka hada da dala $566,754,584, fam 98,526,012 da kuma Naira biliyan 226, da ake bin gwamnatin tarayya.

Tun da farko a ranar Laraba, Shugaban ya rantsar da kwamishinonin tarayya bakwai na hukumar tattara kudaden shiga da kuma kasafin kudi (RMAFC).

Hukunce-hukuncen da Buhari ya yi a cikin mintuna na karshe sun haifar da martani daban-daban, ganin yadda ake kusa da mika mulki ga gwamnatin Bola Tinubu.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, Adesina ya yi magana kan lamarin.

Kakakin shugaban kasar ya ce Buhari na da wa’adin shekaru hudu wanda zai kare a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Ya kara da cewa ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta biya duk wani nau’in bashi da aka ciwo a tsawon shekaru takwas.

“Mugun mutum ne kawai baya biya kuma ba ya bi bashi, abin da littafin kirki ya ce,” in ji shi.

“Sa’ad da ake binka bashi kuma ka ƙi biya, Littafi Mai Tsarki ya ce kai mugu ne.

“Idan ana bin gwamnati duk waɗannan basussukan shari’a, me ya sa ba za ta biya ba? Ya kamata a biya.

“Gwamnati tana da wa’adi daga lokaci zuwa wani lokaci, wa’adin ya kasance daga 2019 zuwa 2023, don haka gwamnati tana aiki.”

Adesina ya kuma yi magana kan kin amincewa da shugaban kasa ya yi na rusa majalisar ministocinsa bayan taron majalisar zartarwar tarayya na karshe a ranar Laraba.

“Ya dogara ga shugaban kasa. Salo ya dace da kowane mutum, wannan shine salon shugaban kasa,” in ji shi.

“Yana son su yi aiki har zuwa ranar ƙarshe. Mun san wasu shugabannin da za su ruguje bayan taron FEC da ya gabata, salon nasu ne.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button