Boko Haram:- An Kashe Wani Angon Soja a Borno.

A Makon da yagabane dai mayakan Boko Haram suka Kashe Sojoji akalla 10, wasu kuma da dama suka Bace.
Cikin Mamatan Hadda wani Jami’in Soja Ango wanda Bai dade da Yin Aure ba Mai Mukamin Laftanar Babakaka Ngorji Ya Rasa Ransa lokacin Harin Kwanton Baunan, Mamacin yana aiki ne a Bataliya ta 202 a Manguno.
Wani Jimi’in Soja ya Shaidawa Yan Jarida cewa…
“Mun rasa sojoji kusan 10 da `yan ta’addan Boko Haram Suka Hallaka, Inji Wani Babban Soja Yace Laftanar. Babakaka Ngorgi ya yi aure kwanan nan. Na halarci bikin aurensa a ranar 7 ga Disamba, 2019 a Maiduguri. Wani babban hafsan sojojin ya shaida wa Jaridar SaharaReporters cewa.
“An kashe sojoji da dama tun bayan da kungiyar Boko Haram ta fara kai hari kan sansanonin soji a shekarar 2018 Inji Shi.
Majiyar ta kara da cewa “A cikin satin daya gabata, mayakan na Boko Haram sun kashe sojoji tare da raunata wasu sojojin Najeriya a biranen Baga, Magumeri, Baga zuwa kan babbar hanyar Kaya da kuma babbar hanyar Maiduguri zuwa Damboa.
Ahmed T. Adam Bagas