Boko Haram: Ka dakko sojojin haya daga kasashen waje don suzo su fatattaki masu tayar da kayar baya, gwamna Zulum ya roki Buhari.
Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nemi taimakon sojojin haya na kasashen waje domin fatattakar kungiyar Boko Haram daga Najeriya.
Zulum ya yi wannan rokon ne yayin da yake karbar tawagar gwamnatin tarayya wadda taje jihar don jajantawa kan kisan gillar da aka yiwa wasu manoman shinkafa a karamar hukumar Jere.
Zulum ya bukaci gwamnatin da Buhari ke jagoranta da ta dauki tsauraran matakai don kawo karshen matsalar rashin tsaro.
Zulum ya kuma bayar da wasu shawarwari ga gwamnatin tarayya kan yadda za a kawo karshen matsalar ‘yan ta’adda.
Ya ce: “Daya daga cikin shawarwarin da muke bayarwa a matsayin hanyoyin da za a iya kawo karshen tayar da kayar baya shi ne shigar da matasanmu cikin gaggawa zuwa aikin soja da na sintiri domin taimakawa kokarin sojojin Najeriya.
“Shawarwarinmu na biyu shi ne shigar da aiyukan makwabtanmu, musamman gwamnatin Chadi, Kamaru da Jamhuriyar Nijar, wajen tsarkake ragowar‘ yan Boko Haram da ke buya a gabar Tafkin Chadi.
Shawarwarinmu na uku shi ne a shigar da aikin sojojin haya don share dajin Sambisa baki daya.
Shawarwarinmu na hudu shi ne a samar wa ‘yan sanda da sojoji, tare da dakaru motoci masu sulke dauke da makamai da sauran kayan aiki masu alaka.”