Tsaro

Boko Haram Na Daukar Sabbin Mayaka, Gwamnonin Arewa Maso Gabas Suka Gayawa Shugaba Buhari

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

A yaune shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin Arewa Maso gabas da kuma shuwagabannin tsaro a fadarsa.

Bayan kammala ganawar, Gwamna Zulum na jihar Borno ya zanta da manema labarai inda yace, sun bayyana shugaba Buhari cewa ya kamata a baiwa ‘yansanda karin makamai dan su rika taimakawa sojoji wajan yaki.

Yace akwai kuma bukatar mutanen dake sansanin ‘yan Gudun hijira su koma muhallansu musamman ma ganin yanda Boko Haram ke amfani da wannan dama tana daukar mayaka.

Yace talauci na taimakawa sosai wajan samun mayakan da Boko Haram take, ya kara da cewa, dan haka suka nemi shugaba Buhari ya samar da yanayin da mutanen da aka kora daga Muhallansu zasu koma su ci gaba da noma da dogaro da kawunansu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button