Labarai

Boko Haram sun kashe mana mutun Dubu talatin da biyar 35,000 sun Kori mutun milyan biyu daga gidajensu ~Gwamnatin Borno

Spread the love

Gwamnatin jihar Borno ta ce sama da mutane 35,000 aka kashe yayin da miliyan biyu suka rasa muhallansu a sakamakon rikicin Boko Haram a jihar.

Shugaban Ma’aikatan na jihar, Farfesa Isah Marte, ya bayyana hakan a Abuja a karshen makon nan lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa ga Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, don neman gwamnatin tarayya ta shiga cikin tsarin samar da kiwon lafiya na jihar.
kawo yanzu ittifaki ya nuna Cewa Jimlar kudin Asarar a arewa maso gabas yakai N9bn kuma jihar Borno ce ta dauki kaso mafi tsoka wato bilyan N6bn.

“Don haka, hakika muna bukatar taimako ba wai kawai daga abokan hadin gwiwa ba har ma daga gwamnatin tarayya.

“Domin sake maido da muhallin da Suka lalace musamman a bangaren kiwon lafiya, asibitoci 11 sun kone kurmus.

“Daya ya kone kurmus, 7 aka lalata, an lalata cibiyoyin kula da lafiya 185.

“Don haka, a bangaren kiwon lafiya, jimillar kayan aiki; asibiti, cibiyoyin kiwon lafiya na farko da aka lalata kamar na 2015, ya kasance 248. Dukda gwamnati ta yi abubuwa da yawa.

“Mun gyara ko gina kusan rabin wadancan gine-ginen har yanzu.

“Muna da ma’aikatan jinya kasa da 1,000 kuma kwanan nan, mun dauki ma’aikatan jinya sama da 360.

Da yake maida martani, Ministan Kiwon Lafiya, Osagie Ehanire ya ce: “Mun damu da abin da ke faruwa a can da kuma yadda za mu iya taimakawa; yadda za mu hada kawunan mu waje guda mu ga yadda za mu rage radadin wahalar da mutane ke ciki. ”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button