Labarai

Boko Haram sun kashe ‘yan Gudun Hijira mutun 50 a Garin Tumur.

Spread the love

Kimanin ‘yan gudun hijirar Najeriya mutun 50 da ke zaune a garin Tumuk na Jamhuriyar Nijar ne suka Rasa ransu Haka Kuma mazauna Yankin na fargabar sake kawo masu wani harin tun bayan da wani hari da wasu da ake zargin’ yan kungiyar Boko Haram ne suka kai musu.

Harin ya faru ne a ranar Lahadi yayin da aka harbe wasu aka kuma kona gidaje

Mafi yawan mazauna garin ‘yan Najeriya ne daga karamar hukumar Abadam ta jihar Borno wadanda suka tsere zuwa makwabciyar kasar ta Nijar.
Akwai ‘yan Nijeriya sama da 40,000 Dake zaune a garin.

A watan Mayun wannan shekarar yawancin ‘yan gudun hijirar sun koma gidajen iyayensu a Abadam bayan irin wannan hari Dake faruwa..

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button