Tsaro

Boko Haram Sun Koma Daukar Yara A Matsayin Mayaka, Rundunar Soji ta yi Gargadi.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Rundunar hadaka ta yaki tsakanin kasahen dake da iyaka da Tafkin Chadi inda ake samun tada kayar baya na Boko Haram sun bayyana cewa kungiyar ta Boko Haram ta fara amfani da yara kanana wajan yaki a matsayin dakaru.

Me magana da yawun rundunar, Col. Timothy Antigha ne ya bayyana haka ga manema labarai daga N’Djamena kasar Chadi a yau, Alhamis.

Yace sun samu wadannan bayananne daga bayanan Sirri dake fitowa daga kungiyar ta Boko Haram.

Sanarwar tace ita kanta Boko Haram ta tabbatar da tana amfani da kananan yara a yanzu a matsayin mayaka idan aka lura da Bidiyon da ta saki na bikin Sallah inda za’a iya ganin kananan yara rike da muggan makamai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button